in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire: 'Yan adawa na dari-dari da shugaban hukumar zabe
2015-09-29 10:42:54 cri
Wani bangaren gungun jam'iyyun adawa dake cikin kawancen kasa domin kawo sauyi (CNC) a ranar Litinin ya nuna kin amincewa da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (CEI) ta kasar Cote d'Ivoire, Youssouf Bakayoko.

A yayin wata zanga zangar adawa da ya shirya, kawancen CNC ya bayyana cewa ba zai halarci zabuka tare da shugban hukumar zabe mai zaman kanta na yanzu ba.

Dokar kasa ta nuna cewa, shugaban hukumar zabe ana zaben shi bisa tsawon shekaru shida kawai, ba wai a kara sake zabensa ba. Youssouf Bakayoko ya yi shekaru shida, sun isa, ba za a sake zabensa ba, in ji Martele Mamadou Koulibaly, kakakin kawancen CNC.

A cewar mista Koulibaly, cigaba da kasancewar mista Bakayoko a kan mukaminsa, take doka ne da kuma kundin tsarin mulki. Dole ne mista Bakayoko ya yi murabus, in ji kakakin CNC.

'Yan Cote d'Ivoire na shirye shiryen zuwa zabuka a ranar 25 ga watan Oktoba mai zuwa, tare da 'yan takarar shugaban kasa goma, wanda ya hada da shugaban kasar mai ci na yanzu Alassane Ouattara.

Kawancen CNC dake kunshe da 'yan takarar shugaban kasa hudu, ya shirya wata zanga zanga domin ganin an daidaita kamfen a kafofin watsa labarai na gwamnati cikin adalci da kwarewa da kuma kawo gyaran fuska ga hukumar zabe. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China