A ranar 2 ga watan Disamban shekarar 2015, adadin wadannan hare hare ya nuna cewa, an kashe sojin MDD guda, da sojojin FARDC bakwai, fararen hula goma da kuma 'dan tawayen ADF guda, in ji mista Amouzoun Codjo Martin, a ranar Laraba a yayin wani taron manema labarai na MDD.
A cewarsa, sojojin MONUSCO suna ci gaba da ayyukan soja a gundumar Arewacin Kivu, tare da hadin gwiwar sojojin FARDC, domin kawar da mayakan ADF. (Maman Ada)