Zambiya na rarraba miliyoyin kwayayen wutar lantarki da ba su shan wuta da yawa
Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Zambiya (ZESCO), ya kaddamar a dukkan fadin kasar wani aikin rarraba kwayayen wutar lantarki da ba su shan wutar lantarki da yawa, bisa wani kokarin taimakawa rage karancin makamashi, in ji wani babban jami'in wannan kamfani a ranar Litinin. Mista Henry Kapala, kakakin ZESCO, ya bayyana cewa kamfanin ya fara aikin rarraba miliyan guda na kwayayen wutar lantarki da ba su shan wuta da yawa a Lusaka, babban birnin kasar, kana wadannan kwayayen wutar lantarki za'a rarraba su a cikin sauran yankunan kasar. Haka zalika, kamfanin na fatan kara shigo da miliyan guda na kwayayen wutar lantarki da ba su shan wuta da yawa domin rarraba su zuwa wasu yankunan kasar domin taimakawa kasar yin tsimin makamashi. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku