in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
China ta yi alkawarin tallafawa sake gina Somaliya, in ji shugaba Mohamoud
2015-12-09 12:15:04 cri

Shugaban kasar Somaliya Hassan Cheikh Mohamoud ya bayyana cewa, takwaransa na kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawarin tallafawa sake gina Somaliya, kasar da yaki ya lalata a tsawon shekaru.

Shugaba Mohamoud ya fadi haka ne a cikin wata hira tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, bayan kammala taron koli na biyu na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika na FOCAC da ya gudana a ranakun 4 zuwa 5 ga watan Disamba a birnin Johannesburg.

Mista Mohamoud ya gana da shugaba Xi a ranar 4 ga watan Disamba a Johannesburg, kafin bude dandalin FOCAC, inda kuma shugabanin biyu suka tattauna batutuwan dake nasaba da dan gantakarsu da kuma sake gina tattalin arziki, ababen more rayuwa da ayyukan jin dadin jama'a a kasar Somaliya, da aka lalata a tsawon shekaru 20 na tashin hankali da suka gabata.

Mista Xi ya yi alkawarin ba da tallafi domin b ada gudunmuwa ga ayyukan sake gina ababen more rayuwa. Haka kuma ya yi alkawarin tura wata tawaga zuwa kasar Somaliya domin kimanta matsalar tsaro da sauran fannonin dake bukatar wani sanya hannun kasar Sin, in ji mista Mohamoud.

Shugaban Somaliya ya danganta kasar Sin a matsayin wata abokiyar hulda mai karfi ta Somaliya.

A ranar 14 ga watan Oktoban shekarar 2014, Sin ta sake bude ofishin jakadancinta a Mogadishu, bayan an rufe shi a shekarar 1991 dalilin barkewar yakin basasa a wannan kasa.

Sake bude ofishin jakadancin na Sin a Mogadishu bayan shekaru 23, na shaida wani muhimmin mataki game da huldar dangantakar kasashen biyu, in ji shugaba Mohamoud.

A cewar shugaba Mohamoud, mista Xi Jinping ya sake nanata niyyarsa wajen tallafawa sake gina Somaliya ta yadda wannan kasa dake kusurwar Afrika za ta kasance wata makomar zuba jari mai kyau. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China