Wakilin musamman na babban magatakardan MDD Nicholas Kay ya yi Allah-wadai da yadda wasu 'yan fashen teku suka yi awon gaba da jirgin ruwan kamun kifi na kasar Pakistan a gabar ruwan Somaliya.
Mr Kay ya ce, ya damu matuka kan yadda ake samun karuwar ayyukan 'yan fashin teku a 'yan kwanakin nan a shiyyar, bayan da aka samu nasarar kawar da matsalar shekaru uku da suka gabata.
Ya ce, wannan matsala na iya gurgunta irin ci gaban da kasar ta Somaliya ta samu bayan farfadowa daga yakin basasa na tsawon shekaru ashirin.
Don haka, Mr Kay ya yi kira ga masu jiragen kamun kifi da su mutunta dokokin kamun kifi na gwamnatin tarayyar Somaliya, sannan su martaba shiyyar cinikayyar kasar da aka kebe.(Ibarhim)