in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta soki harin da aka kai otel din Somaliya
2015-11-03 10:45:20 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar kasashen Afrika AMISOM ta yi allahwadai da harin da aka kai wa wani otel din kasar Somaliya a ranar Lahadi a babban birnin kasar Mogadishu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 12, da wadansu da dama da suka jikkata.

Motocin biyu da aka makare da bam suka fashe a babbar kofar shiga otel din da sanyin safiyar wannan rana, bayan nan kuma maharan suka afka cikin otel din, inda suka yi musayar wuta da masu gadin wajen, wani 'dan kunar bakin wake kuma daya shiga cikin otel din ya tada bam din dake daure a jikin shi.

Sojojin Somliya da na kungiyar AU daga bayan sun isa harabar otel din suka daidaita lamura. Wannan harin dai tuni kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kai shi

A cikin wata sanarwar da aka fitar a Mogadishu a ranar Litinin, tawagar AMISOM ta yaba wa yadda jami'an tsaron Somaliya suka aiwatar da aikinsu da ta bayyana shi a matsayin cikin sauri da sanin ya kamata wanda ya taimaka wa shawo kan lamarin kwarai.

AMISOM ta jaddada bukatar da a ci gaba da hada kai da ba da goyon baya ga gwamnatin Somaliya da sojojinta domin a dakile harin kungiyar Al-Shabaab da take kai wa bayin Allah.

Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohammed shi ma ya soki wannan harin, tare da shan alwashin ganin karshen kungiyar ta Al-Shabaab da kuma inganta tsaro a kasar baki daya.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China