in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka 'yan kungiyar Al-Shabaab 10 a kudancin Somaliya
2015-09-24 10:04:44 cri

Rahotanni daga Mogadishu na kasar Somaliya sun tabbatar da cewar, an hallaka 'yan kungiyar Al-Shabaab su 10 a ranar Laraban nan a wata arangama a yankin Bay dake kudancin kasar.

Abdullahi Sheikh Ahmed, wani babban jami'in soji a yankin ya shaida wa manema labarai cewa, sojojin Somaliya da na Habasha har ila yau sun kone motoci 3 bayan gagarumar arangama da 'yan kungiyar da sanyin safiyar Laraba.

A lokacin arangamar, in ji shi, sun hallaka 'yan kungiyar 10, sannan suka kone wasu motoci, kuma suka kwato yankin mai muhimmanci na Labatan Jirow dake da tazaran kilomita 60 daga birnin Badio a kudancin kasar.

Jami'in sojin ya sanar da cewa, suna rike da 'yan kungiyar ta Al-Shabaab da dama tare da alkawarin gurfanar da su a gaban kuliya.

Wani daga cikin mazauna yankin na Labatan Jirow, Mustaf Jelle ya shaida wa Xinhua cewa, an yi mummunar gwazawa a wannan yankin, inda sojojin gwamnati suka aiwatar da ayyukansu tare da kwato yankin na Labatan Jirow bayan arangama mai tsanani.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China