Gwamnatin kasar Sin za ta lalibo sabbin dabaru da za su taimaka wajen karfafa dangantakar dake tsakanin ta da kasashen Afrika.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Ming, shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Larabar nan, a yayin da yake jawabi a taron manyan jami'an kasar Sin da kasashen Afrika, a shirye shiryen gudanar da dandalin FOCAC, wanda za'a gudanar a ranakun 4 da 5 ga wannan wata a Johannesburg.
Nomaindiya Mfeketo, mataimakin ministan hulda da kasashen waje da hadin kai na kasar Afrika ta Kudu ya ce, kasar Sin da kasashen Afrika za su yi nazari kan hanyoyin da za su karfafa hadin kai da ke tsakanin su, da bunkasa dangantakar da kuma kawancen dake tsakanin su, sannan ya kara da cewar, kasashen na Afrika za su hada gwiwa da kasar Sin, musamman a bangarorin da suka shafi ci gaban masana'antu da samar da ababan more rayuwa da fannin aikin gona na zamani.(Ahmad Fagam)