in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojan Siriya ta musunta mutuwar fararen hula a farmakin da Rasha ta kai
2015-11-30 11:18:57 cri

Rundunar sojan Siriya ta bayyana a jiya Lahadi cewa, Sakamakon binciken da jiragen saman yaki na Rasha su ke gudanarwa a yankunan kasar gabannin kaddamar da farmakin, a don haka tana ganin cewa, farmakin jiragen saman da Rasha ta kai ba zai hallaka fararen hula ba.

Wata majiya daga rundunar sojan ta Siriya ta kara da cewa, kasashen Siriya da Rasha suna kai farmaki ta sama ne ga kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi, wadanda suka yi ikirarin cewa, wadanda da suka mutu sakamakon farmakin fararen hula ne.

A jiya Lahadi, mai ba da shawara kan harkokin waje ga jagoran kasar Iran Ali Akbar Velayati ya bayyana a lokacin da ya kai ziyara a kasar Siriya cewa, a wannan hali da ake ciki, kasar Iran za ta ci gaba da nuna goyon bayanta ga gwamnatin Siriya karkashin jagorancin Bassar Asad. Ya kuma jaddada cewa, wannan aiki ya zama tamkar nauyi ne dake wuyan kasarsa.

Ali Akbar Velayati ya ce, tun bayan samun nasarar juyin juya hali na Islama a Iran, kasar ta Iran da Siriya suka kulla dankon zumunci a tsakaninsu, kuma tun lokacin jagoran kasar Iran Seyyed Ali Khamenei ya tabbatarwa Bashar al-Asad da goyon bayansa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China