Shugabar hukumar zartaswar kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU) Madam Nkosazana Dlamini Zuma ta yi allahwadai da harin da aka kai a jihar Upper Nile da ke Sudan ta Kudu.
Shugabar wadda ta bayyana hakan ranar Talata cikin wata sanarwa, ta bayyana harin na ranar Lahadi da dakarun 'yan tawaye suka kaddamar a matsayin mayar da hannun agogo baya a kokarin da kasashen duniya ke yi na maido zaman lafiya a kasar.
Don haka ta yi kira ga dukkan sassan da abin ya shafa da su martaba yarjejeniyar da aka sanya wa hannu, kana su koma kan teburin sulhu. (Ibrahim)