in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na nuna damuwa sosai game da ci gaban tashin hankali a Sudan ta Kudu
2015-07-27 09:51:09 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta sake jaddada damuwarta sosai kan rikicin Sudan ta Kudu dalilin ci gaban tashe tashen hankali, da kuma hare haren da ake kai wa fararen hula.

Kungiyar AU ta yi wannan sanarwa ne a ranar Asabar bayan kwamitinta na zaman lafiya da tsaro ya samu wani rahoto na kwamitin bincike na AU kan kasar Sudan ta Kudu, tare da tattaunawa wannan matsala a ranar Jumma'a.

Kwamitin ya yi allawadai da babbar murya kan take yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a ranar 23 ga watan Janairun shekarar 2014, da kuma hare haren da ake kai wa kan fararen hula, da ma kungiyoyin agaji.

Haka zalika kwamitin ya nuna rashin jin dadinsa kan ci gaban tirjiya da rashin niyyar siyasa na shugabannin bangarorin dake rikici da juna wajen kokarin samar da hanyoyin da suka dace na kai ga cimma wata yarjejeniyar da za ta taimaka ga kawo karshen rikicin.

Kwamitin zaman lafiya da tsaro ya amince, idan har ya zama dole, da tura dakarun kungiyar a kasar Sudan ta Kudu, in ji sanarwar AU, da ke jaddada goyon bayanta ga tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Sudan ta Kudu (UNMISS). (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China