in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta rantsar da kwamitin binciken kasar Sudan ta Kudu
2014-03-13 10:39:55 cri

A ranar Laraban nan ne kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta rantsar da kwamitin da ta nada domin binciken halin da ake ciki a kasar Sudan ta Kudu a wani biki da aka yi a gaban shugabar kungiyar madam Nkosazana Dlamini-Zuma a cibiyar AU dake birnin Adis Ababa na kasar Habasha.

Ita dai kwamitin binciken, an nada shi ne da nufin duba zargin take hakkin dan Adam da sauran nau'o'in cin zarafi a lokacin tashin hankali tsakanin bangaren gwamnati da na 'yan adawa, in ji AU, wanda sakamakon hakan ne shugabannin kasashen Afrika suka yanke shawarar nada kwamitin binciken a taron zaman lafiya da tsaro da suka yi a watan Disambar bara a Banjul na kasar Gambiya.

Ana sa ran kwamitin binciken zai ba da shawarwari a kan hanyar da ya kamata a bi don kowa ya dauki nauyin dake bisa wuyansa, a kuma samu maslaha ta yin sulhu da yafe wa juna tsakanin al'ummomi mazauna kasar kamar yadda yake a cikin tsarin ayyukan kwamitin.

Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban Nigeriya ne zai jagoranci wannan kwamitin mai mambobi biyar da suka hada da mai shari'a Sophia Akuffo, shugabar kotun kula da hakkin bil adama ta Afrika daga kasar Ghana, sai Mahmoud Mamdani, babban shugaban sashin bincike na jami'ar Makerere daga Uganda, sauran sun hada da wakiliya ta musamman ta AU a kan harkokin mata, zaman lafiya da tsaro, Bineta Diop daga kasar Senegal, da kuma kwamishinan kungiyar ta AU a kan 'yanci da hakkin bil adama Pacifique Manirakiza daga kasar Burundi. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China