Wani sojan Kamaru ya bayyana cewa, an yi fashewar boma bomai a garin Darbhanga na yankin Far-North. A yammacin wannan rana, wani dan kunar bakin wake da ake zaton dan kungiyar Boko Haram ne, ya tada bom a wani matsugunin jama'a, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula uku, tare da dan kunar bakin waken, yayin da mutane da yawa suka ji rauni.
Wani ganau ya bayyana cewa, bayan abkuwar harin ba da dadewa ba, wani dan kunar bakin wake na daban ya tada bom dinsa a wata tashar soja a garin Darbhanga, lamarin da ya haddasa mutuwar dan kunar bakin waken da kuma soja guda.(Fatima)