in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Botswana ya yabawa kamfanin Sin saboda samar da kwarewa ga ma'aikatan kasar
2015-11-27 10:07:58 cri

Mataimakin shugaban kasar Botswana Mokgweetsi Masisi, ya yabawa kamfanin kasar Sin Zhengtai Group, saboda samar da kwarewa ga ma'aikata a kasar.

Mista Masisi, ya yi wannan yabo ne a ranar Alhamis din nan a yayin gabatar da wata gasar nuna fasahar ayyukan hannu da kamfanin ya saba shiryawa sau daya a ko wace shekara, wanda aka gudanar a harabar kamfanin dake Gaborone, helkwatar kasar ta Botswana.

Kamfanin na Zhengtai, ya shafe shekaru da dama yana aiwatar da ayyuka iri dabam dabam a kasar da suka hada da gina katafaren filin wasa na Lobatse, da babban kantin sayar da kaya na Sebele a Gaborone da dai sauransu.

A 'yan shekarun nan kamfanin na Zhengtai, ya sha shirya tarukan ba da horo da shirya gasar musayar fasahar ga ma'aikatan kamfanin 'yan asalin kasar ta Botswana, da kuma raba kyautukan kayayyakin tallafi ga masu karamin karfi a kasar. (Ahmed Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China