in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin ya mikawa BFA tallafin kayayyakin wasa
2015-08-20 09:40:47 cri

Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Botswana ya mikawa hukumar kwallon kafar kasar BFA tallafin kayayyakin wasan kwallon kafa. A cewar mai magana da yawun ofishin jakadancin kasar ta Sin dake Botswana Li Nan, taimakon na wannan karo daya ne kawai, daga matakan karfafa zumunci da ofishin ke gudanarwa.

Da take karbar kayayyakin a madadin hukumar ta BFA, mataimakiyar shugaban hukumar Suzie Montsho ta ce, BFA na fuskantar matsaloli daban daban, wadanda suka hada da rashin isassun kwararru, da masu horaswa, tare da karancin damar daukar nauyi ko kudaden gudanarwa.

Ta ce, hukumar ta yi matukar farin cikin karbar wannan tallafi tare da godiya ga kasar Sin, kuma tallafin ya karfafa gwiwar su. Daga nan sai ta yi kira ga sauran sassan masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tallafawa hukumar ta BFA yadda ya kamata.

Montsho ta kara da cewa, kungiyar kwallon kafar mata ta kasar na samun ci gaba sannu a hankali, duk kuwa da kasancewar kungiya na matakin farko, idan an danganta ta da sauran kungiyoyin kasashe da suke da karfi kwarai.

Yanzu haka dai dangantaka tsakanin kasar Sin da Botswana ta kai shekaru 40, cikin kuma wadannan shekaru, ofishin jakadancin Sin na daukar karin matakai na fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China