in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar ministan harkokin wajen Botswana a Sin na cike da nasarori
2015-07-10 09:50:41 cri

Wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar Sin a Botswana ya fitar, ta ce, ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Botswana Pelonomi Venson- Moitoi ya kai Sin, ta haifar da manyan nasarori ga bangarorin biyu a fannoni da dama.

Sanarwar ta ce, ziyarar ta 'yan kwanakin baya, ta zo a gabar da ake cikin shekaru 40 da kulla dangantakar kawance tsakanin kasashen Sin da Botswana. Kaza lika ziyarar ta zamo wani ginshiki na raya zumunci, kasancewarta ta farko da wani ministan wajen kasar ya kai Sin tun bayan shekarar 1998.

Yayin wannan ziyara, a cewar sanarwar, bangarorin biyu sun tattauna kan dangantakar abota, da harkokin da suka shafi yankuna da na kasa da kasa, musamman masu nasaba da kasashen biyu. Sun kuma cimma matsaya game da shawarwari da dama.

Har wa yau sassan biyu sun amince su hada gwiwa a fannin bunkasa harkokin noma, da kiwon dabbobi, da habaka masana'antun sarrafa kayayyaki. Sauran sun hada da samar da ababen more rayuwa, da inganta kwarewar jama'a, tare da hanyoyin inganta kiwon lafiya.

Bugu da kari Sin ta yaba da kyakkyawar dangantaka da ta dade tana wanzuwa tsakanin kasashen biyu, da kuma kokarin kasar Botswana game da kare rayukan namun daji, tare da hadin gwiwar da take baiwa kasashen duniya wajen cimma wannan buri. A wani mataki na karfafa gwiwar kasar a wannan fanni, Sin za ta samar da kayayyakin kiyaye namun daji da darajar su ta kai kudin RMB miliyan 10 ga kasar ta Botswana, kamar dai yadda sanarwa ta bayyana. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China