in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka da dama ba su cimma nasarorin da ake fata game da muradun karni ba, in ji jami'in UNDP
2015-11-23 10:53:24 cri

Babban mashawarci game da shirin MDD na samar da ci gaba ko UNDP a takaice Neil Boyer, ya ce, da dama daga kasashen Afirka ba su cimma nasarorin da ake fata game da muradun karni ba.

Mr. Boyer wanda ya yi wannan tsokaci yayin babban taro na 38, na dandalin 'yan majalissar kasashen kudancin Afirka, ya ce, kuduri na 8 game da yaki da fatara na muradun karni ya fuskanci kalubale mai yawa. Boyer ya kara da cewa, matsalar rashin daidaito tsakanin maza da mata a fannin guraben ayyukan yi, da rashin managarcin tsarin birane, da karancin tsaftar mahalli, da tsaftacaccen ruwan sha, dukkanin su matsaloli ne dake dada fadada talauci da fatara a tsakanin al'umma.

Kaza lika Boyer ya bayyana cewa, da dama daga kasashen na Afirka sun gaza cimma wasu manyan nasarori a fannin samar da muhalli mai nagarta, tare da samar da a kalla kaso 0.7 bisa dari na kasafin kudaden su wajen samar da ci gaba.

A daya hannun kuma, Mr. Boyer ya ce, duk da wadannan matsaloli, kasashen na Afirka sun cimma nasarar rage mutuwar yara kanana, akwai kuma sauran kalubale game da rage mutuwar mata masu juna biyu, da batun kayyade iyali.

Sauran fannonin da aka samu ci gaba sun hada da batun samar da ilimi kyauta, da inganta rayuwar mata ta hanyar samar musu da damar halartar makarantu. Bugu da kari a cewar sa kasashe irin su Afirka ta Kudu, da Namibia sun taka rawar gani wajen shigar da mata cikin sha'anin jagoranci da siyasa.

An dai bude taron na wannan karo ne a ranar Asabar a birnin Swakopmund na kasar Namibia, za kuma a kammala a ranar Laraba 25 ga watan nan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China