in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gabon da UNDP sun sake daidaita huldar dake tsakaninsu
2013-08-08 15:00:23 cri

Sabon shugaban kwamitin kasar Gabon na yaki da halatta kudin haram da riba, ciki da dukiyar kasa (CNLCEI), Dieudonne Otounga Awassi tare da madam Evelyne Petrus Barry, wakiliyar kungiyar UNDP wato hukumar tsare-tsare da raya tattalin arziki ta MDD dake zaune a kasar Gabon sun dauki niyyar sake habaka dangantakar dake tsakaninsu a ranar Laraba a birnin Libreville. A lokacin wannan ganawa, madam Evelyne Petrus Barry ta gabatar da cigaban aikin da ake samu tare da kwamitin CNLCEI da ya kare wa'adin aikinsa. A cewar wannan jami'ar UNDP dake aiki a matsayin wata gada a cikin wannan hulda, an sanya hannu kan tsarin kasa kan yaki da cin hanci da halatta kudin haram (DSLCCBC) a cikin watan Nuwamban shekarar 2012.

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba a cikin tsinkayensa dai, ya nanata muhimmancin tabbatar da tsarin mulki na gari daga dukkan hukumomi da ma'aikatun gwamnati wajen yaki da cin hanci da rashawa domin karfafa matsayin kasa mai 'yanci da mulki na gari, ta yadda za'a iyar yin rigakafin wannan matsala da kuma yanke hukunci ga masu aikata wannan laifi a kasar Gabon. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China