in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada Haoliang Xu a matsayin mataimakin babban magatakardar MDD na hukumar UNDP
2013-08-14 10:57:55 cri

Wata sanarwa da ofishin kakakin babban magatakardar MDD ya fitar, ta bayyana nadin Mr. Haoliang Xu, 'dan asalin kasar Sin a matsayin mataimakin babban magatakardar MDD Ban Ki- moon, kuma darakatan shiyoyin Asiya da Pacific, a hukumar lura da shirin samar da ci gaba ta MDD UNDP.

Haoliang Xu, wanda kafin nadinsa a wannan sabon mukami, ya taba rike mukamai da dama a hukumar ta UNDP, ciki hadda mataimakin daraktan shiyyar Turai da kasashe renan Ingila, zai maye gurbin Ajay Chhibber daga India, wanda ya yi murabus bisa burinsa na yiwa kasarsa ta haihuwa hidima. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China