Hukumar raya kasa ta MDD UNDP za ta taimaka wa kasashen dake nahiyar Afrika kaddamar da wasu ayyuka masu rage gurbatar iska wadanda hamada ke haddasawa.
Mataimakin darektan hukumar UNDP a Kenya, Fernando Edjang ya ce, kasashen Afrika za su sami tallafi na kudade da fasahohi domin magance matsalar karancin itatuwa da tabarbarewar yanayi.
Mataimakin darektan ya ce, ayyukan za su hada da shuke-shuke kuma tuni hakan ya haifar da ingancin samun kudaden shiga na mata da matasa a kasashen Afrika kudu da Sahara.
Alkalumman kididdiga na nuni da cewar, tabarbarewar yanayi a sakamakon karuwar birane da yawan jama'a ya taimaka wajen asarar dazuzzuka masu itatuwa dake kare muhalli. (Suwaiba)