in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke mayakan Boko Haram 20 a wani samamen soja a Kamaru
2015-11-18 10:34:03 cri

Rundunar sojojin kasar Kamaru ta tabbatar da cewa, ta cafke wasu mambobin kungiyar Boko Haram kusan 20 a yayin da dakarunta suka kai wani samame ta kasa da sama, wanda kuma ya janyo asara ga kungiyar ta Najeriya a ranar Litinin a Ketta, dake yankin arewa mai nisa dake kusa da iyaka da Najeriya.

Tun da sanyin safiyar Litinin, sojojin kasa na rundunar Kamaru suka kaddamar da wani gagarumin samame tare da taimakon hare hare ta sama da jirage masu saukar ungulu domin zakulo gungun mayakan kungiyar ta'addancin da aka sanar da zamansu a wannan yanki na kasar Kamaru, in ji wasu majiyoyin soja. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China