A yau Asabar 14 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon ta'aziyya ga takwaransa na kasar Faransa François Hollande kan hare-haren ta'addancin da suka abku a birnin Paris.
Inda shugaba Xi ya bayyana cewa, ya ji mamaki matuka da abkuwar hare-haren ta'addanci a Paris, wadanda suka haddasa mutuwa da jikkatar dimbin mutane. Don haka, a madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta, da shi kansa, shugaba Xi ya yi tofin Allah tsine da babbar murya kan lamarin, tare da mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu sakamakon lamarin, sannan yana jajanta ma wadanda suka jikkata da duk iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su.
Bugu da kari Shugaban na kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, a ko da yaushe kasar Sin ba ta amince da duk wani matakan ta'addanci da ake dauka ta hanyoyi daban daban ba, kuma Sin na son inganta hadin gwiwa tare da Faransa da ma sauran kasashen duniya a fannin tsaro, domin yaki da ta'addanci, a kokarin kiyaye lafiyar jama'ar kasa da kasa. (Kande Gao)