Shugaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya Mogens Lykketoft da kwamitin sulhu na majalisar sun bayar da sanarwar bi da bi a jiya Jumma'a 13 ga wata, inda suka yi tofin Allah tsine ga hare-haren da aka kai a birnin Paris, babban birnin kasar Faransa da sauran wuraren da ke keyawensa, tare da bukatar da a saki mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da bata lokaci ba.
A cikin sanarwar da ya bayar, Mr. Lykketoft ya furta cewa, duk duniya na bakin ciki matuka da hare-haren da suka abku a birnin Paris, ta'addanci rashin imani ne zalla, al'ummar duk duniya na hadin kai tare da gwamnatin kasar Faransa da kuma jama'arta.
Ya kara da cewa, dole ne a hada gwiwa tare don yaki da irin wannan lamarin tashin hankali masu ban tausayi kuma ba za a yarda da kasancewar irin wannan lamari a zamanin yau ba.
A nasa bangare, kwamitin sulhu ya yi suka mai tsanani kan hare-haren ta'addanci da aka kai a birnin Paris, wadanda suka haddasa mutuwa da jikkatar dimbin mutane, sa'an nan ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda hare-haren suka ritsa da su da ma gwamnatin kasar Faransa.
Kwamitin ya kuma jaddada cewa, dole ne a kama wadannan 'yan ta'adda da kuma gurfanar da su a gaban kotu.(Kande Gao)