in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadun kasar Sin na sashen gandun daji za su ziyarci Kenya kan batun baiwa giwaye kariya
2015-11-10 10:36:04 cri
Tawagar jakadun kasar Sin masu lura da al'amurran gandun daji za ta ziyarci kasar Kenya cikin wannan mako, a wani bangare na shirin yarjejeniya tsakanin Sin da Afrika kan batun kula da namun daji wato CAWA, shirin wanda asusun tallafawa lafiyar dabbobi na kasa da kasa IFAW ya kaddamar a Litinin din nan.

Tawagar jakadun da ake sa ran za su ziyarci Kenyan, sun hada da JC Decaux China da iFENG.com da Beijing MTR Corporation da Shenzhen Press Group da Fulong Media da kuma DEEP magazine.

Daraktan IFAM na shiyyar arewacin Afrika James Isiche, ya ce yana da kyakkyawar fatar shirin na CAWA zai gina wata gada tsakanin Sin da Afrika wajen hada karfi domin tinkarar batun ceto rayuwar giwaye.

Tawagar wacce za ta shafe mako guda, ana sa ran za ta tattauna da jami'an gwamnatin Kenya da suka hada da na ma'aikatar kare muhalli da albarkatun kasa da na ma'aikatar yawon bude ido da kuma na ma'aikatar kula da gandun daji. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China