in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kayayyakin agajin Sin sun isa wurin da girgizar kasa ta afku a Afghanistan
2015-11-04 09:25:21 cri
A ranar Talatan nan, aka yi bikin mika kayayyakin agaji wadanda kasar Sin ta aika wa kasar Afghanistan bayan da ta samu faruwar girgizar kasa. Kayayyakin da kudinsu ya kai kiyasin yuan miliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 1.6 sun isa birnin Kabul ne a ranar jiya Talatan kuma ministan kula da aukuwar bala'u da harkokin jin kai na kasar Wais Ahmad Barmak da jakadan kasar Sin a Afghanistan Yao Jing na cikin wadanda suka shaida mika kayayyakin.
Kayayyakin agajin da za'a rarraba su ga mutanen dake zaune a yankunan da bala'in girgizar kasar ya shafa guda 10, a cewar Mr Wais Barmak, sun hada da barguna 20,000, tantuna 300 da injin din samar da lantarki 60.
An samu aukuwar girgizar kasar mai karfin maki 7.5 a kasar ta Afghanistan ranar 26 ga watan Oktoban da ya gabata wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 115, wassu da dama kuma suka jikkata.
Tun da farko dai a wannan rana mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya sanar da cewar, kasarsa za ta kuma ba da kudin tsaba dala miliyan daya ga gwamnatin Afghanistan domin ta kara hidimar taimaka wa wadanda wannan bala'i ya shafa.
A game da wannan kokari na kasar Sin, minista Wais Barmak ya bayyana matukar godiya saboda saurin kawo dauki da kasar Sin ta fara yi a kasar dake tsakiyar yankin Asiya, yana mai gode wa kasar da al'ummarta baki daya.(Fatimah)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China