in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani harin kunar bakin wake ya kashe mutane 10 a Afghanistan
2015-09-28 10:50:38 cri

An kashe a kalla mutane 10, tare da jikkata 35 bayan wani 'dan kunar bakin wake ya kai hari a ranar Lahadi a filin wasan kwallon hannu na volley-ball a gundumar Paktika a gabashin kasar Afghanistan, in ji wani jami'in kasar.

Fashewar ta faru a wani filin wasannin motsa jiki dake yankin Khair Kot, a yayin da matasa suke wasanninsu da yamma. Dan kunar bakin waken ya tada bom da yake daure da ita a tsakiyar filin, shi ya mutu a yayin harin, in ji wata majiyar wurin. Mutanen da suka mutu da wadanda suka ji rauni an kai su asibitocin dake yankin da kuma babban birnin kasar, in ji wannan majiya, wadda ta kara da cewa, adadin zai iya karuwa ganin cewa wadanda suka jikkata suna cikin wani mawuyacin hali. Kawo yanzu babu wata kungiyar da dauki alhakin kai wannan harin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China