Wasu hare hare ta sama da rundunar sojojin kasar Afghanistan ta kai sun kashe 'yan Taliban 31, wadanda wani babban kwamandan din kungiyar dake cikinsu, tare da jikkata wasu 30 a ranar Lahadi a yankin Musa Kala dake gundumar Helmand a kudancin Afghanistan, in ji kakakin rundunar sojojin Mohammed Rasoul Zazai.
Sojojin saman Afghanistan, tare da taimakon tawagar ba da kariya ta NATO, sun kai wasu jerin hare hare ta sama a ranar Lahadi da safe kan wuraren da 'yan Taliban suka buya a yankin Musa Kala. 'Yan tawaye kusan talatin da daya, wadanda suka hada da wani babban kwamandan, wato Mollah Zarqawi aka kasha, da kuma jikkata 30, in ji mista Zazai. An yi luguden wutar a lokacin da 'yan Taliban suke kokarin kwace yankin Musa Kala. (Maman Ada)