A cikin wata sanarwar hadin gwiwa a birnin Nairobi, kwararru na gungun shawarwari kan binciken noma (CGIAR) sun yi hasashen cewa nan da shekarar 2050, amfanin gona na masara da wake a Afrika zai iya raguwa da kashi 40 cikin 100 dalilin karuwar yanayin zafi. (Maman Ada)