Ana sa ran amfani da kudaden ne wajen taimakawa kasashe masu tasowa wajen bullo da tsarin aikin gona da samar da abinci mai dorewa.
Hukumar FAO ta bayyana cewa, za a yi amfani da wadannan sabbin kudade da kasar Sin ta samar wajen bunkasa musayar dabaru a tsakanin kwararrun kasar Sin a fannin aikin gona, tare da takwarorin su daga kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen dake yankunan tsakiyar Asiya, da tsibiran tekun Pacific, da na nahiyar Afrika, da kuma Latin Amurka wadanda suka fi fama da karancin abinci. (Lami)