Shugaban kasar Guinea mai barin gado Alpha Conde ya kada kuri'arsa a ranar Lahadi da safe a wata mazaba dake a kwalejin Boulbinet, kusa da fadar shugaban kasa, tare da yin amfani da wannan dama domin yin kira ga 'yan kasar Guinea da su yi zabe cikin lumana.
Zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali a birnin Conakry, amma a sauran yankunan kasar kuwa, an fuskanci 'yan matsaloli a wasu rumfunan zabe, dalilin jinkirin da aka samu wajen bude rumfunan zabe da kuma rashin kayayyakin zabe.
Wannan matsala, an fi samun ta a wasu unguwanni dake birnin Conakry, har ma da wasu kananan hukumomin kasar. Akwai inda jami'an zabe ba su je rumfunan zabe ba sai wajen karfe 9 zuwa karfe 10 na safe bisa agogon wurin.
A N'Zerekore, wata karamar hukuma mai nisan kilomita dubu guda daga babban birnin kasar, masu zabe sun fuskanci tafiyar hawainiya wajen fara kada kuri'u. Wasu rumfunan zaben kuma ba a tanadar musu da kayayyakin zabe ba har zuwa kusan sa'o'i goma, a cewar wasu majiyoyi masu tushe. (Maman Ada)