Wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar sojan Najeriyar kanar Sani Usman, ta tabbbatarwa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, rundunar ta kama mutumin da kudi kimanin naira miliyan 1 kwatan kwacin dalar Amurka dubu 5 da wasu kayayyaki.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewar, mutumin shine ke samarwa mayakan kungiyar ta Boko Haram goro da sauran abubuwa musamman masu kara kuzari
Sanarwar tace, an gano mutumin yana kewayawa ne tsakanin Maiduguri da Dikwa-kulli domin neman taimako da zummar tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, amma daga bisani sai ya tura kudaden ga sansanonin mayakan na Boko Haram.
Yayin wani sintiri na hadin gwiwa da rundunar sojin ta kai ranar litinin, ta yi nasarar tarwatsa wani sansanin mayakan Boko Haram a Bulungwa-Naibe dake karamar hukumar Dikwa, kana ta kashe wasu mayakan, sannan ta samu wata motar yaki makare da bindigogin kakkabo jirage, da wasu manyan bindigogi masu sarrafa kansu wadan da 'yan kungiyar ke amfani da su.( Ahmad Fagam)