in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EP ta yi gargadi game da tashin hankalin da zai kunno kai a yankin Chadi
2015-10-09 10:07:09 cri
Majalisar dokokin kungiyar tarayyar Turai ko EP a takaice ta yi kira ga kasashen duniya da su hanzarta daukar matakai don rage tashin hankalin da mayakan kungiyar Boko Haram suka haddasa a Najeriya.

Bugu da kari, mambobin majalisar dokokin kungiyar sun yi kiran da a kara kare kananan yara da kuma ragowar mazauna yankin tafkin Chadi.

A wani kuduri da ya samu amincewar bai daya, mambobin majalisar dokokin sun yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da kungiyar ke kaiwa kan fararen hula.

Ko da a watan Fabrairun da ya gabata ma, MDD ta yi kiyasin cewa, kungiyar ta Boko Haram ta kai hare-haren da ba su gaza 50 ba, baya ga yadda ta ke kashe tare da sace fararen hula a yankunan Najeriya,Kamaru har da Chadi da kuma Nijar.

A don haka majalisar dokokin kungiyar tarayyar ta Turai, ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta hada kai da kasashe makwabtanta don bullo da matakan da za su dakile hanyoyin da kungiyar ke samun kudaden shiga.

Kasar Faransa ta yi kiyasin cewa, a farkon shekarar 2015, Boko Haram tana da dakaru 4,000 zuwa 6,000, yayin da kasashen Amurka da Kamaru suka ce kungiyar tana da dakarun da suka kai 13,000 zuwa 15,000. Koda ya ke zai yi matukar wahala a san hakikanin yawan dakarun kungiyar.

Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Rights Watch ta bayyana cewa, daga shekarar 2009 zuwa shekarar 2014 kungiyar Boko Haram ta halaka fararen hula kimanin 6,000.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China