Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Saliyo Ernest Bai Koroma a jiya Lahadi a birnin New York.
Xi Jinping ya ce, bayan da kasashen biyu suka kulla huldar diplomasiyya, sun goyi baya ga juna kan wasu manyan batutuwan da suka shafi babbar moriyarsu, kuma sun rika taimakawa juna a kai a kai.
Ya kuma kara da cewa, a shekarar bara, kasar Saliyo ta yi fama da cutar Ebola mai tsanani da ba a taba samun irinta ba a tarihi, kasar Sin ta mai da martani wajen ba da taimako cikin gaggawa ga kasar Saliyo. Yanzu dai, kasar Sin na tsara jerin manufofin ba da taimako ga kasashe 3 na Afrika da suka yi fama da cutar Ebola wajen farfaro da zaman al'umma da tattalin arzikinsu.
Kazalika, Xi Jinping ya bayyana cewa, za a yi taron koli na dandalin tattaunawa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a farkon watan Disamba na wannan shekara a kasar Afrika ta kudu. Wannan zai zama taron koli na farko a tsakanin Sin da Afrika da aka kira a nahiyar Afrika, shi ya sa, yana da ma'ana sosai. Kasar Sin ta yi maraba da shugaba Koroma wajen halartar taron.
A nasa bangare, Ernest Bai Koroma ya bayyana cewa, an samu bunkasuwar huldar Sin da Saliyo sosai a shekarun baya. A yayin da jama'ar Saliyo ke kokarin yaki da cutar Ebola, taimakon da kasar Sin ta bayar ya ingiza sauran kasashen duniya wajen mai da hankali da kuma ba da taimako gare ta. Kasar Saliyo za ta ci gaba da kiyaye huldar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma za ta karfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannonin neman samun bunkasuwa da kiwon lafiya da kafa manyan ayyukan more rayuwa, kana za ta yi kokarin cimma daidaito tare da Sin a kan wasu manyan batutuwan kasa da kasa.(Lami)