Shugaba Xi ya kara da cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin yana ci gaba da kasancewa a kan gaba a duniya. A farkon watanni na wannan shekara, saurin bunkasuwar tattalin arikin Sin ya karu da kashi 7 cikin dari, wanda abu ne ba mai sauki ba musamman a halin da ake ciki yanzu da tattalin arzikin duniya ke fuskantar matsaloli.
Kana Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin tana bukatar kara ingancin bunkasuwar tattalin arzikinta, domin daidaita matsalolin rashin daidaito da matsalar dauwamammen cigaba da ake fuskanta a bangaren tattalin arziki, ta yadda za a raya tattalin arzikin kasar ba tare da wata matsala ba a nan gaba.(Lami)