in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya jaddada kara imani da juna da raya hulda iri na sabon salo tsakanin Sin da Amurka
2015-09-25 17:04:25 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama a jiya da dare a masaukin baki na Blair House dake birnin Washington DC.

A wannan rana da yamma, a yayin da shugaba Xi Jinping ya isa birnin Washington DC, ya isa fadar White House don gaisawa da takwaransa na Amurka, Barack Obama.

Inda daga bisani, shugabannin biyu suka tafi Blair House, don tattaunawa har tsawon awoyi 3. A lokacin tattaunawar sun yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan da suka fi jawo hankulansu ciki har da gudanar da harkokin siyasa da huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka. Mataimakin shugaban kasar Amurka Joseph Biden da sakataren harkokin waje na kasar John Kerry da sauran manyan jami'an kasar na daga cikin wadanda suka halarci ganawar.

Da yake jawabi Mr. Xi ya jaddada cewa, bude kofa ga kasashen ketare da yin gyare-gyare a gida ita ce babbar manufar da kasar Sin take bi, kuma za ta ci gaba da inganta bunkasuwar kasar Sin a nan gaba. Ya ce kasar Sin ba za ta rufe kofarta ba, sannan za ta nace ga neman bunkasuwa cikin lumana, wannan shi ne abin da aka gada daga tarihi da kuma halin da ake ciki.

A nasa bangare, shi ma shugaba Barack Obama ya ce, kasar Amurka ta yi maraba da bunkasuwar kasar Sin, ba ma kawai hakan ya dace da moriyar jama'ar Sin ba, hatta ma ya dace da moriyar kasar Amurka da kuma kasashen duniya. Ya yi nuni da cewa, kasashen Amurka da Sin sun ba da misali wajen tinkarar kalubale tare, inda suka cimma nasarar yin hadin gwiwa kan batun sauyawar yanayi da kuma taimakawa kasashen Afrika wajen yaki da cutar Ebola. A cewar shi kasashe da dama na saurin bunkasa a duniya, don haka, ya kamata a kara wakilcin kasar Sin da kuma sauran kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa a duniya. Barack Obama ya tabbatar da cewar, kasar Amurka tana fatan kasar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa kan batutuwan duniya.

Har illa yau, shugabannin kasashen biyu za su yi shawarwari a yau Jumma'a domin kara yin musayar ra'ayi.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China