Mr. Xi ya bada hujjojin ne a tattaunawarsa da shugaban Amurka kuma mai masaukin bakin shi Barack Obama a fadar White House.
A cikin hujjojin yace bangarorin biyu ya kamata su cigaba da musaya na kut da kut tare kuma da hulda da juna a kowane mataki. Manyan tsarurukan dangantaka kamar tattaunawa na dabaru da tattalin arziki da kuma matakin koli na tuntubar juna tsakanin al'ummomi ya kamata a kara basu damar taka rawar a zo a gani.
Kasashen biyu ya kamata su fadada tare da zurfafa hadin gwiwwar dake tsakanin su a sassa daban daban da su ka hada da tattalin arziki,ciniki, aikin soji, yaki da ta'addanci,kafa dokoki,makamashi, muhalli da ababen more rayuwa..
Shugaban na kasar Sin ya ce Sin da Amurka ya kamata su inganta musayar al'umma tsakanin su tare da fahimtar muhimman bangarorin huldar zumunci.
Kasashen biyu har ila yau ya kamata su mutunta banbancin dake tsakanin su a tarihi, al'adu, gargajiya da tsarin zamantakewa har ma da hanyoyin cigaba, sannan su yi koyi da junan su.
Bangarorin biyu har ila yau su zurfafa tattaunawa da hadin gwiwwa a al'amurran da suka shafi yankin Asia da fasifik.
Sannan yace su tunkari kalubalolin da suka shafi yankuna da ma duniya tare, su karfafa dabarun inganta zumuncin su su kuma samar da wani al'umma na duniya mai kunshi da kayayyakin bukata ga kowa.(Fatimah Jibril)