Mr.Xi Jinping ya kuma gabatar da jawabi a makarantar, inda ya ce, ilmi shi ne kashin bayan ci gaban kowa ce kasa da kuma al'ummarta, kuma lokacin kuruciya shi ne lokaci ne mafi daraja a rayuwar mutum. Don haka, ya yi fatan daliban za su mayar da hankali ga harkokinsu na karatu, don aza harsashi mai inganci ga makomarsu. Ban da haka, ya yi fatan matasa na Sin da na Amurka za su hada kansu, don ciyar da huldar da ke tsakanin kasashen biyu gaba zuwa wani sabon matsayi.(Lubabatu)