in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarki Salman na Saudiya ya bukaci a tabbatar da matakan tsaron a gun aikin hajji
2015-09-25 10:53:25 cri

Mahajjata sama da 700 ne suka mutu kana sama da 800 kuma suka jikkata, sakamakon wani turmutsutsu da ya auku a garin Minna dake da nisan wasu kilomitoci da birnin Makka na kasar Saudiya. Yayin da musulamai kimani miliyan 2 daga sassa daban-daban na duniya da ke halartar aikin hajjin bana ke kan hanyar su ta zuwa wurin jifa daga filin Arfa.

Don haka, sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na kasar Saudiya ya bukaci hukumomin gwamnatin kasar da su kawar da kalubalolin tsaro dake shafar aikin hajjin, domin hana sake aubkuwar irin wannan hadarin a nan.

Sarkin ya bayyana haka ne a yayin da ya gana da shugabannin rundunar tsaron kasar, inda ya bayyana bacin ransa dangane da hadarin da ya auku a wannan rana, ya kuma bukaci a gudanar da bincike kan hadari yadda ya kamata, da kuma sanar da sakamakon bincike ga jama'a cikin sauri.

Babban jakadan kasar Sin dake birnin Jeddah na kasar Saudi Arabiya ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana jiran bayani daga gwamnatin kasar ta Saudi Arabiya, a sa'i daya kuma tawagar aikin hajji da ma'aikatan ofishin jakadanci suna bincike ko akwai Sinawan wannan hadari ya rutsa da su da ke kwance a asibitoci, ya zuwa yanzu, babu wani labarin cewa akwai mahajjatan kasar Sin da suka rasu ko suka ji rauni sanadiyar wannan hadari ba.

A ranar Asabar 26 ga wata ne ake fatan kammala aikin hajjn na bana. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China