in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman ta shugaban kasar Sin ta gana da firaministan kasar Mauritania
2014-08-05 15:18:13 cri
Manzon musamman ta shugaban kasar Sin Xi Jinping kuma shugabar hukumar kidayar jama'a da tsara iyali ta kasar Sin Li Bin ta gana da firaministan kasar Mauritania Moulaye Ould Mohamed Laghdaf, inda Laghdaf ya jajantawa gwamnatin kasar Sin da jama'arta game da girgizar kasar da ta faru a gundumar Ludian dake lardin Yunnan, inda Li Bin ta nuna godiya da wannan jaje

Li Bin ta bayyana cewa, akwai dadadden zumunci tsakanin kasar Sin da ta Mauritania, kuma kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan wannan zumunta tare da fatan kasashen biyu za su ci gaba da fadada hadin gwiwa a tsakaninsu a dukkan fannoni ciki har da kiwon lafiya.

A nasa bangare, Laghdaf ya yaba wa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, sannan ya nuna godiya ga kasar Sin bisa ga taimako da goyon bayan da ta ke baiwa kasar Mauritania, da kuma yadda Sin ta tura rukunonin likitoci zuwa kasar don kula da lafiyar jama'ar kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China