in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na taka rawa ga ci gaban duniya, in ji Li Keqiang
2015-09-10 10:26:21 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana tafiya a matakin da ya dace, kuma ya taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Firmaminista Li ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da mutumin da ya kirkiro dandalin tattalin arzikin duniya Klaus Schwab da kuma shugabannin 'yan kasuwa na duniya, gabanin taron Davos na shekara-shekara da zai gudana a birnin Dalian da ke lardin Liaoning na kasar Sin.

Ya ce, kamata ya yi daukacin kasashen da tattalin arzikinsu ke tangal-tangal su fito da wani tsari da zai bunkasa tattalin arzikin duniya a nan gaba, ta yadda za a gudu tare a tsira tare.

Li ya ce, kasashen da suka ci gaba sun ci gajiyar hadin gwiwar kasa da kasa da kasar Sin ta kirkiro, kuma hakan zai taimakawa shirin kasashe masu tasowa na bunkasa masana'antunsu wanda daga karshe zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin duniya.

Firmanista Li ya kuma bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da hukumomin kasa da kasa wajen raya kasuwannin kasar Sin, ta yadda sauran sassa za su amfana.

A nasa jawabin, Schwab ya ce, yadda dandalin na Davos ke kara yin tasiri wata alama ce ta yadda kasashen duniya ke nuna tabbaci kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. Ya kuma bayyana kudurinsa na kara yin hadin gwiwa da kasar Sin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China