Za a gudanar da taron dandalin tattalin arzikin duniya WEF na shekara 2015 a Davos dake kasar Switzerland domin magance manyan matsalolin dake addabar duniya.
Taron wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 21 zuwa 24 ga Watan Janairu da muke ciki, zai samu halarci baki fiye da 2500 daga kasashe fiye da 140, wadanda za su wakilici gwamnatocinsu, wasu kuma za su wakilci kamfanoni na 'yan kasuwa da kungiyoyi masu zaman kansu na duniya, da malaman jami'a da kuma masu kare hakkin bil'adama da kafofin watsa labarai.
Taron zai mai da hankali wajen magance matsaloli na yanayi da na karancin arziki, tare da tunkarar matsaloli na rashin ayyukan yi da maganar saka jari, da samar da daidaito na ma'aikata mata da maza, tare da yaki da cin hanci da rashawa da sauran matsaloli dake addabar duniya.
A yayin da yake jawabi ga manema labarai, shugaban dandalin WEF Klaus Schwab ya ce, duniya ta canza, saboda haka ma ya sa taken taro ya kasance "sabon tsari na duniya". (Suwaiba)