in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu 'yan siyasar Jamus sun zargi yammacin duniya da kasancewa dalilin matsalar 'yan gudun hijira
2015-09-07 11:03:04 cri

Wasu 'yan siyasa na jam'iyyun adawa a kasar Jamus sun zargi kasashen yammacin duniya da kasancewa musabbabin matsalar 'yan gudun hijira da a halin yanzu da tarayyar Turai take fuskanta.

Kasar Jamus na fuskantar kwarar 'yan gudun hijira mafi girma inda mutane dubu 800 suke neman takardar zama a wannan shekara a lokacin da kasashen na tarayyar suke fama da babbar matsalar 'yan gudun hijira tun bayan yakin duniya na biyu.

Yawancin 'yan gudun hijira da suka isa Jamus sun fito daga yankunan dake fama da yake yake.

Kasashen Turai a karkashin jagorancin Amurka sun hirgiza wadannan yankuna da dama, lamarin da ya hadasa kafuwar kungiyoyin ta'addanci, da ma kwashen albarkatun wadannan yankuna, in ji Sara Wagenknecht da Dietmar Bartsch, shugabannin gungun 'yan majalisu na jam'iyyar adawa ta Die Linke a cikin wata jaridar da za'a fito a ranar Litinin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China