Akwatin nadar bayanai na jirgin Germanwings ya shaida aniyar mataimakin matukin jirgin na kada jirgin
Masu gudanar da bincike, na hukumar sanya ido ga harkokin kiyaye hadurran jiragen sama na kasar Faransa ko BEA a takaice, sun ce bayanan dake kunshe cikin akwatin nadar bayanai na biyu, wanda aka samo cikin tarkacen jirgin saman kamfanin Germanwings wanda ya yi hadari, sun nuna cewa da gangan mataimakin matukin jirgin ya kada shi cikin tsaunuka.
Mahukuntan kasar Faransa sun tabbatar da hakan a Jumma'ar nan, cikin wata sanarwa da aka sanya a shafin yanar gizon hukumar ta BEA, bayan gudanar da wani bincike kan akwatin nadar bayanan.
Faduwar wannan jirgi mai lamba A320 cikin tsaunukan Alps a kudancin kasar Faransa, ya ritsa da rayukan mutane 144, da kuma ma'aikatan jirgin su 6. (Saminu Hassan)