in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saliyo ta yabawa Sin saboda rage adadin sojojinta
2015-09-06 12:02:47 cri

Babban mataimakin jami'i mai magana da yawun gwamnatin kasar Saliyo Abdullahi Baraytay ya ce, gwamnatin kasarsa ta jinjinawa kasar Sin dangane da gudanar da kasaitaccen bikin tunawa da samun nasarar yakin kin harin zaluncin Japanawa shekaru 70 da kuma matakin da kasar Sin ta dauka na rage kimanin dubu 300 na adadin sojojinta.

Baraytay ya bayyana hakan ne a yayin hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a ranar Juma'ar nan, ya ce, wananan gaggarumin biki ya gwadawa duniya irin jajurcewa da kuma sadaukar da kai da alummar kasar Sin suka nuna a gwaggwarmayar kwatar 'yancin daga harin cin zali, kuma hakan ya taimaka wajen kawo karshen mulkin danniya, har ma a kasashen nahiyar Afrika baki daya.

Da yake karin haske dangane da matakin da kasar Sin ta dauka na rage sojojin ta dubu 300, Baraytay ya ce, wannan mataki ya nuna wa duniya a fili cewar, Sin kasa ce mai son zaman lafiya, musamman idan aka yi la'akari da yadda wasu kasashen duniya ke ta kokarin kara yawan sojojinsu, amma kasar Sin kokarin rage adadin sojojin ta yi, ya ce, wananan mataki abin yabo ne.

Kazalika ya bukaci kasashen duniya da su jinjinawa kasar Sin saboda shirya wannan gaggarumin biki na cika shekaru 70 don tunawa da kawo karshen harin cin zali. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China