Shugaban kasar Saliyo Renest Bai Koroma a ranar Alhamis din nan ya kaddamar da wani ginin da kasar Sin ta yi na dakin gwajin zamani na kwayoyin cuta da sauran abin da suka jibanci kiwon lafiya a kasar.
Da yake magana wajen kaddamar da wajen ya ce, a wannan rana sun shaida babban ci gaba a cibiyar hana yaduwar cututtukan kasar wanda ba kawai zai amfanar da al'ummar Saliyo ba ne har ma yankin baki daya.
Ya yaba wa kasar Sin cewar, ba kawai tana samar da kayayyakin kiwon lafiya ga kasar ba, har ma ta yi alkawarin koyar da ma'aikatan wajen yadda za su tafiyar da na'urorin lokacin da za'a damka musu a hannun su gaba daya. Shugaba Koroma ya ce, wannan wani sabon babi ne a bangaren kiwon lafiya wanda kasar ta samu babban koma baya dalilin barkewar annobar Ebola a wannan shekarar.
A nashi jawabin, jakadan kasar Sin a Saliyo Zhao Yanbo, ya ce, Sin ba kawai tana mai da hankali a kan ba da taimako ga annobar Ebola da ake fama da shi yanzu ba ne, har ma tana kokarin ganin ta inganta bangaren kiwon lafiyar kasar baki daya. Gina wannan dakin gwajin cututtuka na daya daga cikin ayyukan da Sin yi niyya, sannan ya yi fatan wajen zai taimaka wa kasar ta Saliyo don inganta sha'anin kiwon lafiyarta da samar da kariya daga cututtuka. (Fatimah)