in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane sama da 200 sun mutu sakamakon gobarar da ya tashi a gidan mai a Ghana
2015-06-05 11:07:51 cri

Ministan harkokin cikin gidan kasar Ghana Mark Woyongo ya shaidawa manema labaru a jiya Alhamis cewa, yawan mutane da suka rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta tashi a wani gidan mai dake Accra, babban birnin kasar ya wuce 200.

A daren ranar Laraba ne, wani abu da ake zaton bam ne ya fashi a wani gidan mai dake tsakiyar birnin Accra, inda ya haddasa wata mummunar gobara. Minista Woyongo ya ce, a yanzu haka ana ci gaba da yin bincike don gano musabbabin hadarin.

A jiya kuma shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya kira taron gaggawa na majalisar ministocin kasar. Bayan taron ne kuma ya sanar da cewa, tun daga ranar 8 ga wata za a fara makoki na tsawon kwanaki uku. Ban da wannan kuma, yanzu haka gwamnatin kasar ta samar da cedi miliyan 60, wato kimanin dalar Amurka miliyan 15 ga wadanda masu ji rauni da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

A wannan rana shi ma ministan kiwon lafiyan kasar Ghana ya yi kira ga jama'ar kasar da su yi kokarin ba da gudummawar jini don ceton mutanen da suka ji rauni.

Wadanda suka ganewa idanunsu sun gayawa manema labaru cewa, mai yiwuwa gobarar ta tashi ne sakamakon wutar da ta hadu da man da ya malala a kasa.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake tafkawa a birnin Accra ya kawo cikas ga harkokin sufurin jama'a, wannan ya sa mutane da yawa suka nemi mafaka a wannan gidan mai a wannan lokaci shi ya sa aka samu asarar rayuka da dama. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China