in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Ghana na son ganin ta karfafa hadin gwiwwa da kasar Sin
2015-07-04 13:38:58 cri

Ministan harkokin wajen kasar Ghana Madam Hanna Serwah Tetteh tace kasar na sa ran karin hadin gwiwwa da kasar Sin ganin yadda dangantakar diplomasiyya a tsakanin su ta cika shekaru 55 a wannan watan na Yuli.

Tace an samu nasararorin daga dangantakar hadin gwiwwa a cikin wadannan shekaru 55, ta hanyar zuba jari daga kasar Sin a gwamantoci da hukumomi masu zaman kansu a wassu manyan ayyukan a kasar.

Da take hira da kamfanin dillanci labarai a birnin Accra, Madam Hanna Tetteh tace ayyukan kamar na matatar samar da iskar gas na Atuabo da kuma madatsar ruwa na Bui da kamfanonin kasar Sin suka yi aikin su sun habaka cigaban tattalin arzikin kasar. A cewar ta hadin gwiwwa tsakanin kasashen biyu ya kai wani babban mataki a cikin 'yan shekarun baya bayan nan tare da samar da sakamako masu armashi a bangarori daban daban musamman bayan kafuwar dandalin tattaunawar hadin kan kasashen Afrika da Sin.

A daren ranar alhamis din nan ne dai ofishin jakadancin kasar Sin dake Ghana yayi liyafar cika shekaru 55 da kulla dangantakar diplomasiya a tsakanin kasashen biyu, wanda ya samu halartar Ministan harkokin ilimin kasar Ghana Jane Naana Opoku-Agyemang da sauran manyan jam'ian kasar, jami'an diplomasiya, dalibai da wakialn al'ummar Sinawa mazauna kasar ta Ghana.

A cikin jawabinta wajen liyafar jakadar kasar Sin a Ghana Sun Baohong tace tana da imanin cewa muddin bangarorin biyu suka cigaba da aiki tare suna hadin gwiwwa za'a iya ingiza dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba a kuma samu sakamako mai kyau da gamsarwa a wani shekaru 55 masu zuwa sannan za'a gina wata dangantaka tsakanin kasashen biyu da zai zama abin nuni na dangantakar Sin da kasashen Afrika. An dai kulla dangantakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da Ghana ne a ranar 5 ga watan Yuli na shekara ta 1960

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China