Mataimakin babban sakataren MDD Jan Eliasson ne ya bayyana hakan jiya Litinin a cibiyar MDD dake birnin New York yayin da yake halartar bikin nune-nunen hotuna game da tunawa da cika shekaru 70 da kawo karshen harin Japanawa, da yaki da ra'ayin masu nuna karfi a duniya da kuma kafuwar MDD.
Da ya ke tsokaci game da bikin faretin da kasar Sin za ta shirya, Eliasson ya bayyana cewa, babban sakataren MDD Ban Ki-moon zai halarci bikin saboda muhimmancin ranar 3 ga watan Satumba. Ban yana fatan wannan biki ya kasance wata dama ta koyi da abubuwan da suka faru a tarihi, da kuma yin imani da shimfida zaman lafiya bisa tushen tsarin mulkin MDD a nan gaba.
Hakazalika kuma, Eliasson ya ce, Sin muhimmiyar kawar MDD ce, yana fatan kasar Sin da MDD za su ci gaba da yin hadin gwiwar a nan gaba. (Zainab)