in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yaba kokarin kasar Sin na tinkarar sauye-sauyen yanayi
2013-11-20 21:20:55 cri
A yayin taron sauye-sauyen yanayi da aka gudanar a birnin Warsaw dake kasar Poland, babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya gana da jagoran tawagar kasar Sin kuma mataimakin kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Xie Zhenhua, inda Ban Ki-moon ya nuna yabo ga kokarin kasar Sin na tinkarar matsalar sauyin yanayi.

Ban Ki-moon ya kuma yabawa kasar Sin da Amurka bisa cimma daidaito kan batun rage fitar da abubuwan dake gurbata muhalli da bulla da matakan tinkarar matsalar sauyin yanayi. Wannan ne misali mai kyau na manyan kasashe masu karfin tattalin arziki suka yi hadin gwiwa wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi.

A nasa bangare, Xie Zhenhua ya bayyana cewa, kasar Sin kasa ce mai tasowa dake daukar nauyin dake bisa wuyanta, tana kuma taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China