Shugaba Xi ya bayyana cewa, kasashen Sin, Rasha da Mongoliya, kasashe ne da ke makwabtaka da juna, kuma sun kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, kana akwai harsashi mai kyau wajen inganta hadin gwiwar bangarorin, baya ga makoma mai haske dake tsakaninsu. Ya ce ya kamata a yalwata hadin gwiwa ta fannoni uku bisa manyan tsare-tsare kuma cikin dogon lokaci tsakanin sassan.
A cewar sa abu na farko shi ne, batun tabbatar da amincewar juna a fannin siyasa, da kafa gamayya tsakanin su. Kana, sai batun hada dabarun raya kasashen uku, da ingiza hadin gwiwar tattalin arziki na shiyya-shiyya. A karshe kuma akwai batun inganta mu'amala tsakanin jama'a, da inganta hadin gwiwar bangarorin uku.
Game da batutuwan duniya da na shiyya-shiyya kuwa, shugaba Xi ya bada shawarar inganta tuntubawar juna da shawarwari, don kiyaye zaman lafiya da karko a duniya da kuma shiyya-shiyya.
A nasa bangare kuwa, Shugaba Putin cewa ya yi, tun fara shawarwari tsakanin shugabannin kasashen 3 a bara, sassan da abun ya shafa daga kasashen 3 sun inganta mu'amala, da hadin gwiwa a fannin gina hanyoyin jiragen kasa da yawon shakatawa. Ya kuma bayyana farin cikin sa da cimma daidaito game da karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a yayin shawarwarin, matakin da a cewar sa ya dace da moriyar dukkan kasashen 3.
Haka kuma, shugaban Elbegdorg ya ce, an cimma daidaito game da karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a yayin taron koli karo na 2 na kasashen uku, ya kuma gamsu da hadin gwiwar kasashen uku a fannonin gina hanyoyin jiragen kasa da sufurin kaya, da amfanin gona, da haka ma'adinai da ababen more rayuwa, wanda zai kawo alheri ga jama'ar kasashen uku.(Bako)